Shugaban riko na jam’iyyar APC na kasa, Alhaji Ali Bukar Dalori, ya karbi ragamar mulki tare da yin alkawarin tabbatar da gaskiya da hada kai da gudanar da ayyuka tare da hadin kai tare da dukkan yayan jam’iyyar..
Dalori wanda shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa shiyyar Arewa maso Gabas, kafin nadin nasa, ya yi alkawarin ne yau Litinin a Abuja a wani taro da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa NWC.
Kamfanin Dillancin Labara i na Najeriya NAN, ya ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci Dalori da ya jagoranci shugabancin jam’iyyar ta APC biyo bayan murabus din da shugabanta na kasa Dakta Abdullahi Ganduje ya yi a ranar Juma’ar da ta gabata.
Ganduje, a cikin takardar murabus dinsa da ya mika wa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa NWC ta hannun sakatarenta na kasa, Sanata. Ajibola Basiru, ya ce, ya na bukatar lokaci don kula da lafiyarsa da sauran batutuwan da suka shafi kansa.
Tsohon gwamnan jihar Kano Ganduje, ya karbi shugabancin jam’iyyar APC ne a watan Agustan shekarar 2023.
Ya gode wa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa NWC bisa ci gaba da goyon bayansu da biyayyarsu, inda ya ce ba ’yan mambobi ba ne kawai, abokan hadin gwiwa neda ke bada hadin kai da gudunmawa wajen saita alkibar jam’iyyar.
Ya yi alkawarin ba da goyon baya ga ajandar sake fasali da shugaba Tinubu ya dauki aniya ya na mai cewa, Renewed Hope Agenda ba kawai taken yakin neman zabe ba ne, amma taswirar hanya ce mai rai wadda ta riga ta magance muhimman kalubale a fannin tattalin arzikinmu tsaro da hadin kan kasa.
Dalori, ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar APC da masu ruwa da tsaki da su ci gaba da kasancewa da hadin kai, ya na mai cewa sauyin siyasa yakan haifar da rashin tabbas, amma kada a bari ya haifar da rashin hadin kai a tsakaninsu.
Ya yi alkawarin jan ragamar ‘ya’yan jam’iyyar zuwa tafarki madaidaici da za ta jagorance matsayinsa na shugaban riko zuwa tsawon lokain da zai rike ta.













































