Gwamnatin tarayya ta jaddada matsayarta cewa za ta dakatar da biyan kuin tallafin man fetur nan da ƙarshen watan Yuni mai zuwa.
Ministar Kuɗi Zainab Ahmed ta faɗa yayin gabatar da tanadin kasafin kuɗi na 2023 ranar Laraba cewa gwamnati ta ware naira tiriliyan 3.36 ne kawai don biyan tallafin a wata shidan farko na sabuwar shekara.
A cewarta, matakin ya yi daidai da sanarwar da aka bayar tun a 2022 ta ƙarin wa’adin cire tallafin zuwa wata 18.
Da take fayyace ƙunshin kasafin kuɗin, ministar ta ce kuɗin shigar da Najeriya ta samu zuwa Nuwamban 2022 sun kai naira tiriliyan 6.5, abin da ke nufin ƙasar ta samu ƙarin kashi 87 cikin 100 na hasashen abin da za ta samu a shekarar.
Cikin kuɗaɗen da aka tara sun ƙunshi wanda gwamnatin tarayya ta tara na biliyan N586, hukumar kwastam ta karɓi naira biliyan 15, cibiyoyin karɓar haraji masu zaman kansu sun tara tiriliyan 1.3, sai kuma sauran sashe-sashe da suka tara tiriliyan 3.7.













































