Cikin Hotuna: Gwamnan Kano ya bayyana ba tare da Jar Hula ba bayan sauya sheƙa zuwa APC

IMG 20260227 WA0009 720x430

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana a ƙasar Faransa ba tare da jar hularsa ta alama ba, lamarin da ya janyo hankalin jama’a tare da haifar da muhawara.

SolaceBase ta ruwaito cewa gwamnan, wanda aka gani sanye da kaya masu sauƙi ba tare da hular gargajiyar da aka fi danganta shi da ita ba, ya bayyana hakan ne ba da daɗewa ba bayan sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

IMG 20260227 WA0014 768x1264

Wannan ne karo na farko da aka gan shi a bainar jama’a ba tare da jar hular ba tun bayan komawarsa jam’iyyar mai mulki.

Sai dai duk da cewa sabon bayyanar tasa ta jawo ce-ce-ku-ce, ba shi ne karo na farko da hakan ya faru ba.

IMG 20260227 WA0009 2

A wasu lokuta da suka gabata, Gwamna Yusuf ya taba bayyana ba tare da jar hula ba yayin ziyararsa a Saudiyya da wasu wurare, inda shi ma ya sanya kaya masu sauƙi.

Duk da haka, masu bibiyar harkokin siyasa sun ce fitowarsa a Faransa na da wata ma’ana ta musamman, duba da lokacin da hakan ya faru, wato bayan sauyin jam’iyyarsa.

IMG 20260227 WA0010

Jar hular dai an daɗe ana kallonta a matsayin wata alama da ta shafi hotonsa a idon jama’a da kuma martabarsa ta siyasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here