BUK ta fara binciken wasu zarge-zargen cin zarafi da damfara ta Internet da ake yi akan wani dalibi

BUK BUK New

Jami’ar Bayero da ke Kano BUK ta bayyana cewa ta lura da zarge-zargen da ke yawo a cikin rubuce-rubucen jama’a da kuma a kafafen sada zumunta da ke alakanta wani mutum da ake cewa dalibi ne a jami’ar da aikata kwaikwayon wani mutum a internet da kuma badakala ta kudi.

A cikin wata sanarwa da Daraktan harkokin hulda da jama’a na jami’ar, Lamara Garba, ya fitar ranar Laraba, ya bayyana cewa mahukuntan jami’ar na son sanar da cewa jami’ar Bayero da ke Kano na da tsauraran ka’idoji kan halayya, ladabtarwa da kuma dabi’ar dukkan dalibai a tsawon lokacin karatunsu.

Sanarwar ta kara da cewa duk wata dabi’a da za ta iya bata sunan jami’ar ko kuma ta lalata martabarta ana daukarta da matukar muhimmanci.

Sanarwar ta kuma jaddada cewa halayen kashin kai na kowane dalibi ba sa wakiltar dabi’u ko martabar jami’ar Bayero da ke Kano a matsayin cibiyar ilimi.

Dangane da zarge-zargen da ake yi, jami’ar ta fara wani bincike na farko domin gano gaskiyar abin da ya faru.

Mahukuntan jami’ar da suka dace suna duba lamarin ne bisa ka’idojin jami’ar da kuma hanyoyin ladabtarwa da suka shafi halayen dalibai.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa wani malamin aikin jarida a jami’ar Kennesaw State da ke Atlanta a kasar Amurka, Farfesa Farooq Kperogi, kwanan nan ya wallafa a shafinsa na kafafen sada zumunta inda ya bayyana wani da ake zargi da damfara wanda ya yi ikirarin cewa dalibi ne a jami’ar Bayero da ke Kano, kuma ya nemi taimako daga gare shi domin biyan kudin makaranta.

Rahotanni sun ce Farfesan ya rika taimaka masa tsawon shekaru kafin daga baya ya gano cewa sunan da aka ba shi ba na gaskiya ba ne, kuma wanda ake zargin yana kwaikwayon wata mace ne.

Bayan wallafar sakon, wasu mutane da dama sun fito suna bayyana yadda wannan mutumin da ake zargin ya damfare su ta irin wannan hanya.

Mahukuntan jami’ar sun kuma yaba da kokarin Farfesa Farooq Kperogi da sauran mutane masu kyakkyawar niyya da ke taimaka wa dalibai masu bukata ta hanyar biyan kudin rajista da sauran kudaden karatu.

Jami’ar ta tabbatar wa jama’a cewa idan bincike ya tabbatar da zarge-zargen, za a dauki matakin ladabtarwa da ya dace bisa dokokin jami’ar da kuma dokokin da suka dace.

Sannan jami’ar ta bukaci jama’a da su bari binciken da ake yi ya kammala, tare da kaucewa yada jita-jita ko bayanan da ba a tabbatar da su ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here