Shugankasa mai barin gado, Muhammadu Buhari a yau Juma’a ya zagaya da zababben shugaban kasa Bola Tinubu cikin Villa domin ya ga yacce gidan yake.
Shugaban kasan ya zaga da Tinubun ne bayan sun idar da saallar juma’a a masallacin Villa dake garin Abuja, kafin su fara zagayawa cikin gidan, inda ya kai shi zauren majalisar zartaswa (Council Chambers) da kuma Press Gallery.
Bayan nan Buharin ya kashi offishin da shugaban kasa yake zama, zauren walima da kuma inda shugaban kasa dashi da iyalen sa suke zama a fadar.
Shugaban kula da harkokin tafiye-tafiyen shugaban ƙasa, Lawal Kazaure, ne ya yiwa Tunubun bayani guraren ya yin zagayen.













































