Wata Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa belin da aka bai wa tsohon Babban Lauyan Tarayya (AGF), Abubakar Malami, a baya ya daina aiki, sakamakon sake miƙa shari’ar ga wata sabuwar alkaliya.
Kotu ta bayyana cewa tun da an fara sauraron shari’ar daga farko a gabanta, dukkan matakan da aka ɗauka a baya, ciki har da belin da Mai shari’a Emeka Nwite ya bayar sun zama ba su da inganci, don haka sai an sake neman beli a hukumance.
A baya dai EFCC ta shigar da tuhume-tuhume guda 16 kan tsohon AGF, bisa zargin wankiyar kuɗi da mallakar kadarori ba bisa ka’ida ba da darajarsu ta haura Naira Biliyan 8.7.
A zaman kotun na baya-bayan nan, mai gabatar da ƙara, J.S. Okutepa, ya bayyana halartar sa tare da roƙon a karɓi amsar tuhuma daga waɗanda ake ƙara kan sabuwar tuhumar mai ƙunshe da guraben laifi 16.
Malami, ɗansa Abdulaziz da matarsa Asabe sun musanta dukkan tuhume-tuhumen da aka sabunta.
Bayan an karɓi amsar tuhumar, masu gabatar da ƙara sun roƙi kotu ta sanya ranar fara shari’a.
Sai dai lauyan masu kare kai, J.B. Daudu (SAN), ya roƙi kotu da ta ci gaba da amfani da sharuddan belin da Mai shari’a Nwite ya bayar a baya, yana mai cewa Kotun Tarayya kotu ɗaya ce, kuma an riga an ba su beli.
A martanin da ya bayar, mai gabatar da ƙara ya amince cewa an taba ba da beli, amma ya ce sabuwar kotu na da ikon ko dai ta amince da tsoffin sharuddan ko kuma ta sanya sababbi.
Ya ƙara da cewa duk da ba zai matsa lamba kan batun ba, amma ya kamata kotu ta sanya sharuddan da za su tabbatar da halartar waɗanda ake ƙara a shari’a.
Tun da farko dai sharuddan belin sun haɗa da biyan Naira Miliyan 500 kowannensu, tare da tsayawa da mai tsaya musu guda ɗaya wanda dole ya mallaki kadara a Maitama ko Asokoro.
Haka kuma an buƙaci su miƙa fasfo ɗin su na ƙasashen waje guda biyu kowannensu ga kotu, sannan a tabbatar da adireshin masu tsayawa musu ta hannun Mataimakin Babban Magatakardar Kotu.
A hukuncin da ta yanke, Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta ce duk lokacin da aka fara shari’a daga farko sakamakon sake miƙa ta, dukkan matakan da aka ɗauka a baya sukan rushe a idon doka.
Lauyan masu kare kai ya amince cewa babu takardar neman beli a hukumance a gaban kotun, amma ya nemi a yi roƙon baka.
Kotu ta ƙi amincewa da hakan, tare da umartar su da su shigar da takardar neman beli a rubuce kuma su kai wa masu gabatar da ƙara, sannan za a ba da gajeriyar ranar sauraro.
Haka kuma masu kare kai sun sanar da kotu cewa sanya ranar fara shari’a na iya haifar da matsala domin waɗanda ake ƙara na farko da na biyu na hannun DSS kuma ba a iya tuntuɓar su.
Kotu ta ce ba za ta yi hasashe kan matsayin kowanne ɓangare ba, tare da jaddada cewa alhakin tabbatar da halartar waɗanda ake ƙara na kan masu gabatar da ƙara.
Sai dai masu gabatar da ƙara sun ce waɗanda ake ƙara ba sa hannunsu, kuma ba za su iya tilasta DSS ta kawo su ba.
Daga nan Mai shari’a Abdulmalik ta ɗage shari’ar zuwa ranar 6 ga Maris domin sauraron buƙatar beli da kuma fara shari’a.
Ta kuma bayar da umarnin a tsare Malami da ɗansa a Gidan Yari na Kuje, yayin da aka umarci a tsare matarsa a Gidan Yari na Suleja.













































