Majalisar Ɗinkin Duniya za ta buɗe wani babban taro da za a baje-kolin mutum-mutumi iri daban-daban masu amfani da fasahar ƙirkirarriyar basira ranar Alhamis a Geneva.
Ƙungiyar Harkokin Sadarwa ta Duniya ITU ce ta ɗauki nauyin taron, wanda zai mayar da hankali kan yadda za a yi amfani da ƙirƙirarriyar basira wato AI wajen tallafa wa aikin Majalisar Dinkin Duniya da inganta rayuwa da kuma sauƙaƙa wa al’umma.
Za a nuna mutum-mutumi da yawa da suke da ƙwarewar kwaikwayon fikirar ɗan’adam ta fuskar taimakawa don gudanar da wasu ayyuka a ma’aikatu.
Sai dai saɓanin fargabar cewa mutum-mutumi mai aiki da ƙirkirarriyar basira na iya haifar da illolin da za su haddasa rashin aikin yi ga ɗan’adam, taron zai samar da wasu dokoki da za su ƙayyade ayyukan fasahar.
Gagga-gaggan kamfanonin sadarwa na duniya irinsu Google da Amazon da Microsoft, da sauran ƙwararru a fannin fasahar sadarwa da wakilan gwamnatoci ne za su albarkaci taron.












































