An kashe jami’ai 15 a wani harin kwantan ɓauna a Sudan ta Kudu

Sudan Ta Kudu, kashe, jami'ai
Akalla mutum 15 da suka haɗa da manyan jami'ai ne aka kashe a wani harin kwantan bauna da aka kai a Sudan ta Kudu. Jami'ai sun ce kwamishinan gundumar Boma...

Akalla mutum 15 da suka haɗa da manyan jami’ai ne aka kashe a wani harin kwantan bauna da aka kai a Sudan ta Kudu.

Jami’ai sun ce kwamishinan gundumar Boma da ke Pibor yana dawowa ne daga wata ziyara da ya kai wani ƙauye ranar Talata, lokacin da wasu matasa daga wata unguwa da ke gaba da juna suka kai hari .

An kashe shi ne tare da masu tsaronsa da mataimakin kwamandan sojojin Boma.

Karin labari: Nijar ta gargadi kungiyoyi masu zaman kansu da su ringa bin ka’ida

Yarjejeniyar zaman lafiya ta 2018 ta kawo ƙarshen yaƙin basasa na shekaru biyar a Sudan ta Kudu.

Amma yankuna da dama ciki har da gundumar Boma sun fuskanci ɓarkewar rikicin kabilanci.

Waɗannan hare-haren ramuwar gayya ne na hare-haren da ake kai wa shanu, da suka hada da kabilun Murle da Anyuak da Nuer da Dinkas.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here