Ademola Lookman ya goge bayanan ƙungiyar Atalanta daga shafinsa, tare da daina bin ƙungiyar bayan samun saɓani da Kocinsa

LB OP lookman 750x430

Ɗan wasan ƙungiyar Super Eagles, Ademola Lookman, ya fusata game da makomar sa a ƙungiyar Atalanta bayan ya daina bin ƙungiyar a shafin Instagram tare da goge duk wasu bayanai da suka shafi ƙungiyar daga shafinsa, kwanaki kaɗan bayan saɓanin da ya samu da Kocinsa, Ivan Juric.

Rikicin ya auku ne a lokacin wasan da Atalanta ta doke Olympique Marseille da ci 1–0 a ranar Laraba, lokacin da Lookman ya nuna fushi bayan an cire shi daga wasa a minti na 75.

Hotunan talabijin sun nuna lokacin da Juric ya riƙe hannun ɗan wasan yayin da suke musayar maganganu kafin jami’an ƙungiyar su shiga tsakani don kwantar da hankali.

Bayan wasan, kocin ƙungiyar ya bayyana cewa wannan lamari abu ne da ke faruwa a cikin wasanni, inda ya ce wasu ‘yan wasa ba sa farin ciki idan an cire su daga wasa, amma ana warware irin haka a cikin ɗakin sauya kaya.

A taron manema labarai da ya biyo bayan haka a ranar Asabar, Juric ya sake jaddada cewa an warware batun, yana mai cewa Lookman ɗan wasa ne mai kuzari kuma babu wata matsala tsakaninsu.

Sai dai daga baya, an lura cewa Lookman ya cire duk wani abin da ya shafi ƙungiyar daga shafinsa na Instagram, tare da daina bin ƙungiyar gaba ɗaya.

A bara ma, ɗan wasan mai shekaru 28 ya yi irin wannan mataki bayan ƙungiyar ta ƙi amincewa da tayin fam miliyan 50 daga ƙungiyar Inter Milan, wanda hakan ya sa bai halarci atisayen bazara ba.

Yayin da ake tunkarar lokacin canjin ‘yan wasa a watan Janairu, ana ganin Lookman na iya neman barin ƙungiyar Atalanta sakamakon sake bayyana rashin jituwa tsakaninsa da Kocin.

Lookman, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen lashe kofin Europa League tare da ƙungiyar a bara, bai samu irin wannan nasara ba a wannan kakar wasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here