ADC da NNPP na yaɗa bayanan ƙarya kan Dokar Zaɓe ta 2026 – Fadar Shugaban Ƙasa

Bayo Onanuga 1024x576 1 750x430

Fadar Shugaban Ƙasa ta gargadi jam’iyyun adawa da abin da ta kira yaɗa bayanan ƙarya game da sabuwar Dokar Zaɓe ta 2026 da kuma gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin APC.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai taken cewa ya kamata jam’iyyun adawa su daina yawan koke-koke da ɓacin rai marar tushe kan Dokar Zaɓe da gwamnatin APC.

Onanuga ya ce wasu jiga-jigan adawa, ciki har da ‘yan jam’iyyar ADC da NNPP, sun yi zarge-zarge kan Shugaba Bola Tinubu da gwamnatin tarayya, yana mai cewa zarge-zargen na yaudara ne kuma an yi su ne domin ɓata sunan Majalisar Tarayya da gwamnati.

A cewarsa, sabuwar dokar ta tanadi aikewa da sakamakon zaɓe kai tsaye (real-time transmission), tare da amfani da fom EC8A a matsayin madadin idan aka samu matsalar sadarwa.

Ya ƙara da cewa dandalin IReV ba cibiyar tattara sakamako ba ce, illa dai hanya ce ta ɗora sakamakon domin jama’a su gani.

Fadar shugaban ƙasa ta kuma kare tanadin zaɓen fidda gwani ta hanyar kai tsaye (direct primaries) da kuma tsarin maslaha (consensus) wajen zaɓen ‘yan takara a jam’iyyu.

Onanuga ya ce cire tsarin wakilai (delegate-based primaries) zai ƙarfafa dimokuraɗiyyar cikin gida tare da mayar da ikon jam’iyya ga mambobinta.

Ya musanta zargin cewa Majalisar Tarayya ta yi watsi da ra’ayin ‘yan ƙasa, yana mai cewa an shafe sama da shekara biyu ana tattaunawa da masu ruwa da tsaki da ƙwararru kafin a amince da gyaran dokar.

Haka kuma ya yi watsi da zargin cewa gwamnati na yunƙurin kafa jam’iyya ɗaya, yana mai cewa Najeriya na ci gaba da kasancewa ƙasa mai tsarin jam’iyyu da dama, inda ake da fiye da goma sha biyu da aka yi wa rijista.

Ya buƙaci jam’iyyun adawa da su daina yawan koke-koke da zanga-zangar da ba ta da tushe kan sabuwar dokar, yana jaddada cewa gyaran dokar ya ƙarfafa tsarin zaɓe tare da rufe giɓin da ke cikin tsohuwar dokar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here