Bayan shafe shekaru 10 ba tare da ta dau gasar kasar Italiya ba, tawagar AC Milan na dab da lashe kofin a karon farko.
Nasarar da kungiyar ta yi akan abokiyar karawar ta Atlanta da ci 2-0, a ranar Lahadi 15 ga Mayu 2022, a filin wasa na Sansiro dake Milan, ta hannun ‘yan wasa Rafeal Leao da Theo Harnandez, ya sa kungiyar na neman canjaras ko nasara a wasan ta na karshe da Sassalou ta lashe gasar.
Ƙungiyar ta Milan, ta shafe tsawon shekara 10 rabon ta da daukar gasar tun bayan da ta lashe lokacin tsohon mai horar da tawagar Massimiliano Allegri, a shekarar 2010/11.
Sai dai mafarkin kungiyar ka iya samun tasgaro matukar ta yi rashin nasara a wasan ta na karshe , matukar abokiyar hamayyar ta Inter Milan ta samu galaba a wasan ta na karshe.
Yanzu haka Milan tana da maki 83, kana ta farko a teburin gasar inda Inter Milan ke biye mata a baya da maki 81.












































