Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Adekunle Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Asabar 25 ga watan 2023 da kuri’a miliyan 8,794,726.
Tsohon matainmakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ne ke biye masa da kuri’u miliyan 6,984,520.
Sai kuma dan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi wanda ya samu kuri’a miliyan 6,101,533.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya zo na hudu da kuri’u miliyan 1,496,687.
Kusan za a iya cewa wannan ne sakamakon zaben da ya fi kowanne daukar dogon lokacin kafin a sanar da shi a baya-bayan nan sakamakon dalilai da dama.
Jam’iyyun adawa na PDP da LP sun ce ba za su karbi sakamakon ba bisa zargin tafka magudi a mazabu da dama, inda kuma suka ce za su garzaya kotu.













































