‘Yan sanda a Canada sun kama wasu ‘yan Najeriya biyu – Gbemisola Akinrinade and Adebowale Adiatu – kan tuhumar sun azurta kwunansu da kudaden damfarar wasu matafiya bayan sun sayar musu da tikitin jiragen sama wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka 500,000.
Galibin matafiyan da suka sayi tikitin jiragen saman daga yankin Calgary suke kuma jiragen da suke son shiga sun taso daga nahiyar Afirka ne, kamar yadda ‘yan sandan yankin Peel suka sanar.
Hukumomin ‘yan sandan sun ce ana tuhumar mutanen biyu da damfarar matafiya da mallakar kadarorin da ba nasu ba ne, da yaudara da kuma amfani da na’urar komfuta da niyyar cutar da jama’a.
Sun kuma bukaci matafiya su mayar da hankali soosai kan sahihancin shafukan intanet din da suke mu’amula da su.













































