Wasu ‘yan bindiga sun farwa wata mujami’ar garin Kabba na jihar Kogi a yau Lahadi, inda suka kashe mutum guda tare da awon gaba da mutane biyu.
maharan sun je mujami’ar ta yankin Okedayo dake kan hanyar Kabba zuwa Okene ne da misalin karfe 10:15 na safiya, yayin da harkokin ibada suka fara gudana.
Kakakin ‘yan sandan jihar Kogi, DSP William Aya, ya tabbatar da aukuwar lamarin, wanda ya bayyana a matsayin abun takaici, yana mai cewa ‘yan sanda za su farauto ‘yan bindigar tare da tabbatar da sun fuskanci hukunci.
Wani mutum Kayode Akanbi, dake mujami’ar a lokacin aukuwar lamarin, ya ce maharan sun isa ne jim kadan bayan fara harkokin ibada.
Karanta Wannan: YANZU-YANZU: Tsohon Mataimakin Gwamnan CBN, Obadiah Mailafia ya rasu
Ya kuma shaidawa kamfanin dillancin labarai na NAN ta wayar tarho cewa, maharan su 6, na dauke ne da bindigogi da adduna, kuma ba su lullube fuskokinsu ba.
“mun fara addu’a kenan, ina fassara kalaman Pasto, sai kwatsam suka shigo ta babbar kofa, suna daga bindigogi”.
“sun yi ta harbin kan mai-uwa-dawabi, inda mutane suka fara gudun neman tsira”.
A cewarsa, mutanen biyu da maharan suka sace, su ne mafi manyanta a mujami’ar. Haka kuma yayin harin, sun kashe wani mutum mai shekaru 45, yayin da matar daya daga cikin mutanen da aka sace da kuma wani mutum na daban, suka ji rauni.
Kayode Akanbi, ya ce daga bisani ‘yan sanda sun je wurin da lamarin ya auku inda suka kai mamatan wajen adana gawarwaki na babban asibitin Kabba, yayin da suka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa Lokaja, domin samun jinya.
Idan za a iya tunawa, ko a ranar Lahadi, 12 ga watan Satumba, wasu ‘yan bindiga sun kai hari cibiyar gyaran hali ta Kabba, inda suka saki fursunoni 240, kuma kawo yanzu, ba a kai ga gano 114 daga cikinsu ba.














































[…] Wannan: Kogi: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Guda Tare da Awon gaba da Mutum 2 a […]