Gabanin zaben 2023, wata kungiyar arewa dake bin diddigin shugabanci na gari ta yi kira da a tsige shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa Farfesa Mahmood Yakubu.
Kungiyar ta yi barazanar kai karar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Majalisar Dokoki ta kasa, Ofishin Jakadancin tarayyar turai kan gazawar Shugaban Hukumar INEC na yin murabus ko kuma a kore shi.
Jaridar SOLACEBASE a makon da ya gabata ta rawaito cewa gamayyar jam’iyyun siyasa suka bankado wani shirin karkashin kasa da ake na tsige shugaban hukumar zaben.
Gamayyar kungiyoyin jam’iyun a wani taron manema labarai ta zargi APC da shirin tsige Farfesa Mahmood Yakubu daga mukaminsa.
Shugaban kungiyar Arewa Citizens’ Watch Alhaji Mohammed Adamu a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kaduna a karshen mako, ya zargi shugaban hukumar zaben da tawagarsa dayin wasarairai tareda nuna ganganci da nufin cin karensu ba babbaka don kawai murkushe masu zabe a yankin arewa a 2023.
Adamu ya kuma dage cewa dole ne shugaban hukumar ta INEC da tawagarsa su tashi haikan don ci gaba da gudanar da babban aiki na gudanar da zabe mai inganci da gaskiya a 2023.













































