Hukumar Raya Kasashen Najeriya da Faransa sun rattaba hannu kan yarjejeniya bada tallafin Yuro miliyan 25 don aikin samar da wutar lantarki a kasar.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa kungiyar Tarayyar turan da kuma AFD ne ke daukar nauyin shirin a tsukun arewacin Najeriya yayin da Kamfanin tunkudo wutar lantarki ke gudanar da aikin.
Sanarwar tace an Sanya Hannun ne don ƙarfafa ƙarancin haɓakar tattalin arziƙin sinadaran Carbon a yammacin Afirka ta hanyar inganta ingancin wutar lantarki a Najeriya tare da tallafawa bunƙasa kasuwar wutar lantarki a yankin ƙarƙashin tafkin wutar lantarki na yammacin Afirka.
Da yake jawabi a wajen rattaba hannu a Abuja, Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare na Kasa, Clement Agba, ya ce aikin ya yi daidai da manufofin shirin raya kasa na 2021 zuwa 2025.
“Ina so in godewa tarayyar turai da kuma gwamnatin Faransa bisa dafawa fannin samar da wutar lantarki a Najeriya musamman yadda ya shafi layukan sadarwa da tashoshin sadarwa.
A nasa bangaren, Manajan Daraktan TCN, Mista Sule Abdulaziz ya godewa gwamnatin Faransa da tarayyar turai bisa goyon bayan da suke baiwa Najeriya.
A cewarsa, Aikin a Yankin Arewa yana da matukar muhimmanci ga hukumar domin zai inganta zaman kuzarin lantarki da kuma shirin fadada kamfanin.
Abdulaziz ya tabbatar wa dukkan bangarorin gudanar da ayyukan cikin nasara.
Anasa tsokacin jakadan Faransa a Najeriya, Emmanuelle Blatmann ta bayyana cewa, Faransa ta yi farin cikin matuka na tallafawa wannan aiki, domin hakan ya nuna kyakkyawar alakar dake tsakanin Najeriya da Faransa da kungiyar EU.
Blatmann ta ce tana alfahari da abin da AFD ke yi a Najeriya, domin a cikin shekaru tara da suka wuce Faransa ta zuba jarin kusan dala biliyan 3 tare da gudanar da ayyuka 40 a sassa daban-daban.
A cewarta, kasar Faransa ta kuma kuduri aniyar taimakawa Najeriya wajen cimma matsayar ta kan sauyin yanayi bisa yarjejeniyar Paris.












































