Matashi ya kashe mahaifinsa mai shekaru 90 kan katin cire kudi na ATM a jihar Kwara

wp content uploads 2020 08 Police arrest man for Sodomy
wp content uploads 2020 08 Police arrest man for Sodomy

Matashin mai shekara 23 ya makure mahaifinsa nasa wanda tsohon soja ne, har sai da ya mutu, a Jihar Kwara.

Kafin ya yi wannan aika-aikan, sai da ya yi wa dattijon allurar Farasitamol hade da wasu sinadaran kisa.

Hakan ne ya sa dattijon ya galabaita ba ya iya yin komai, inda shi kuma yaron ya dauke shi a kan wani babur da ya aro zuwa banki, domin sabunta masa katin ATM dinsa da kuma lambar sirri.

Jami’in yada labarai na  ’yan sandan Jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya ce bayan nan ne matashin ya dauki tsohon zuwa wani kangon gini ya makure shi ya kashe shi.

“Daga nan ya haka rami ya binne dattijon sannan ya tsere zuwa Jihar Kaduna, inda ya yi amfani da katin ATM din ya cire N59,000 daga asusun bankin dattijon,” in ji shi.

Ya ce matashin ya shaida wa ’yan sanda masu bincike cewa ya yi hakan ne saboda ya samu lambar sirri katin na mahaifinsa.

Da ya samu kuma sai ya ga ba shi da bukatar mahaifin nasa, don haka ya yanke shawarar kashe shi.

Kakakin ’yan sandan ya bayyana cewa an kuma gano cewa matsahin ya sayar da babur din da ya aro, kuma an kwato shi daga inda ya sayar.

Aminya

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here