Majalisar Dattawa na yunkurin haramta tikitin masu addini iri guda a takara

national assembly
national assembly

Dan majalisar Dattawa mai wakiltar Kogi ta yamma a zauren majalisar Sanata Smart Adeyemi, ya gabatar da kudirin doka da ke neman kawo karshen tsayar da ‘yan takara masu addini irin guda a matsayin shugaban kasa da mataimakin sa.

Adeyemi, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja ranar Lahadi, ya ce akwai bukatar a yi watsi da batutuwan da ake ta cece-kuce kan batun tsayar da ‘yan takara masu addini daya da jam’iyyun siyasa za su yi bayan zaben shugaban kasa na 2023.

Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya rawaito cewa kudirin da Sanatan ya gabatar na da taken:

“Kudirin doka don gyara dokar Zabe ta 2022 da sauran abubuwan da suka shafi dokar.”

Adeyemi ya ce kudirin da ya mika yana neman gyara sashi na 84 na dokar ta hanyar shigar da sabon sashe (3) cikin baka.

A cewarsa karamin sashe na 3 da aka gabatar ya kunshi cewa:

“Babu wata jam’iyyar siyasa da za ta tsayar da ‘yan takara masu addini daya a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa bayan wa’adin wannan zango.’’ in ji Adeyemi.

Adeyemi ya ce yana goyon bayan matsayar kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) kan batun tikitin Musulmi da Musulmi, da har yanzu ake ci gaba da tattaunawa akai.

Sai dai ya ce yana goyon bayan tsayawa takarar Sanata Bola Tinubu da Kashim Shettima a matsayin ‘yan takarar jam’iyyar APC a zaben 2023, duba da irin yadda suke gudanar da ayyukansu da kuma tsarin tafiyar da mulki.

Adeyemi ya yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da addini ba, da su ga fitowar Tinubu da Shettima a matsayin nufin Allah.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here