Mutane 6 Sun Makale yayin da wani gini mai hawa Bakwai ya rufta a Legas

COLLAPES BUILDING
COLLAPES BUILDING

Kimanin mutane shida ne suka makale a cikin baraguzan ginin bene mai hawa bakwai da ya ruguje kusa da titin Sand Field, da ke unguwar Lekki a jihar Legas.

Majiyoyi sun ce ginin da ake ginawa ya rufta ne da sanyin safiyar Lahadi.

Kodinetan Hukumar ba da Agajin gaggawa ta Kasa, (NEMA), a yankin na jihar Legas, Ibrahim Farinloye, shi ne ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Lahadi.

Farinloye ya ce, “Gini mai hawa bakwai ya ruguje a titin Sand field dake Lekki. An ce mutane shida sun makale kuma tuni masu ba da agaji sun karasa wajen.”

Babban Sakatare na Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas, Olufemi Oke-Osanyintolu, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.

Yayin da yake mayar da martani kan lamarin, ya ce jami’an hukumar da isar su sun gano cewa ginin mai hawa bakwai ana kan aikinsa ne a lokacin da ya rushe.

Oke-Osanyintolu ya ce, “Babu wani wanda ya samu rauni. Sai dai rahotanni sun ce kimanin mutane shida ne suka makale a karkashin baraguzan ginin da ya ruguje.

“Za a kawo kayan aikin tona gini masu inganci na hukumar domin ceto wadanda suka makale.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here