Sheikh Ibrahim Khalil ya zama Dan Takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar ADC

IMG 20220523 WA0005 678x381 1
IMG 20220523 WA0005 678x381 1

Shahararren malamin addinin musulunci Sheikh Ibrahim Khalil ya zama takarar gwamnan Jihar Kano a karkashin jam’iyyar ADC.

Jaridar Solacebase  ta rawaito cewa Sheikh Khalil, wanda ya fito takarar ba tare da hamayya ba, an tabbatar masa da takarar ne yayin wani taro na musamman da jam’iyyar gudanar ranar Lahadi a Jihar Kano.

Yanzu haka dai Malam Ibrahim Khalil, zai fafata da Yan takara na sauran jam’iyyun Siyasa masu neman kujerar Gwamnan Kano, ciki har da APC da PDP a zabe Mai zuwa.

Da yake mika wa Sheikh Khalil, fom din tsayawa takarar gwamna a jam’iyyar ADC a gidan Mumbayya da ke Kano, shugaban jam’iyyar na kasa Ralph Okay Nwosu ya bayyana cewa an tabbatar da Sheikh Khalil zai rike tutar jam’iyyar ADC a zaben gwamna na shekarar 2023 mai zuwa duba da rikon amanar sa.

Shugaban jam’iyyar na kasa wanda ya bayyana manufar jam’iyyar a kan gaskiya da mutunci, ya jaddada cewa Sheikh Khalil, ya cancanta ya yi Gwamnan Kano a Jam’iyyar ADC.

Ya kuma bada tabbacin shirin Jam’iyyar ADC na cika alkawarin bawa mata kashi 35 cikin 100 na mukaman siyasa da kuma karfafa gwiwar matasa don cimma burinsu na rayuwa.

Ralph, ya kuma bukaci matasa, Maza da mata da su yi taka tsan-tsan da manyan jam’iyyun siyasa, inda ya tunatar da su cewa bada kudi a siyasa ba zai magance matsalolin kasa ba.

A yayin da yake bayyana nadamar abin da ya dauka a matsayin almubazzaranci da dukiyar kasa da aka yi na tsawon shekaru goma, Ralph ya kalubalanci ‘yan Najeriya da su yi watsi da yaudarar jam’iyyun APC da PDP da ke mulki wanda ya yi ikirarin cewa jam’iyyarsu ta ADC zata kai Najeriya tudun mun tsira.

Ya ce ADC za ta ci gaba da karfafa gwiwar matasan Najeriya da matan don bawa manyan jam’iyyu mamaki a babban zaben 2023.

Da yake jawabi bayan samun amincewar jam’iyyar, dan takarar gwamnan jam’iyyar ta ADC, Sheikh Ibrahim Khalil, ya yi alkawarin tabbatar da adalci da bin doka matukar aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar Kano.

Sheikh Khalil, wanda tsohon dan takarar gwamna ne a jam’iyyar PDP, kafin ya koma APC, daga bisani kuma ya koma ADC, ya yi alkawarin ba da fifiko kan harkokin ilimi, kiwon lafiya, ci gaban matasa da kuma bunkasar tattalin arziki, inda kuma ya sha alwashin karbar mulki a Jihar Kano.

Shugaban jam’iyyar ADC na kasa tun farko ya kaddamar da shugabannin zartarwar jam’iyyar na shiyyar Arewa maso Yamma, tare da tsohon kwamishinan kudi na Kano Farfesa Kabiru Dandago a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa kuma shugaban shiyyar Arewa maso Yamma da sauransu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here