Malami ya magantu kan  ayyana tsayawa takarar gwamna a 2023

Abubakar Malami 1
Abubakar Malami 1

Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN bai bayyana sha’awar tsayawa takara a zaben 2023 ba.

Dokta Umar Jibrilu Gwandu, mataimakin na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja a ranar Talata 5 ga Afrilu, 2022.

Sanarwar ta ce bayanin ya zama dole duba da yadda wasu kafafen yada labarai ke yada labarin karya.

A cewar sanarwar, shelanta tsayawa takara a siyasance ba wai wani boyayyen al’amari ne ko kuma wani aiki na sirri da wani sashe na kafafen yada labarai ke iya yadawa ba.

Ya ce rahoton ya samo asali ne saboda sha’awar da mabiya suka nuna na son ya tsaya takarar.

Sai dai ya mika godiyarsa ga magoya bayan Ministan da sauran jama’a da suka nuna sha’awarsu.

Gwandu ya ce, inda lokaci ya yi za’a ji daga bakin ministan ta kafafen yada labarai da suka dace.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here