Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi ga shugabanta Farfesa Joash Amupitan ya yi murabus, tana mai bayyana irin waɗannan buƙatu a matsayin hari ga ‘yancin kanta da kundin tsarin mulki ya tanada.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a daren Alhamis a Abuja, babban sakataren yaɗa labarai na INEC, Adedayo Oketola, ya bayyana cewa kalaman da wasu ‘yan siyasa ke yi na zargin son zuciya ga shugabanta ba su da tushe, inda ya ce hakan ya biyo bayan matakin da hukumar ta ɗauka na bin umarnin hukuncin kotun daukaka kara.
Sanarwar ta bayyana cewa INEC wata hukuma ce da kundin tsarin mulki ya kafa, inda nadin mukami, wa’adin aiki da kuma cire shugabanta da kwamishinonin ƙasa duk suna gudana ne bisa doka.
Ta kara da cewa shugaban hukumar ba ya rike da mukami ne bisa son zuciyar kowace jam’iyya ko wata kungiya, tare da cewa duk wani kira na a cire shi ba tare da bin tsarin doka ba kai tsaye hari ne ga ‘yancin hukumar zaɓe.
INEC ta bayyana cewa ta bi hukuncin kotun daukaka kara ne domin kaucewa sake faruwar irin abubuwan da suka faru a jihohin Zamfara da Plateau, inda aka tube zababbun jami’ai bayan hukumar ta saba wa umarnin kotu, tare da cewa kin bin umarnin babbar kotun tarayya zai iya kawo cikas ga shari’o’in da ke gudana.
Hukumar ta kuma yi watsi da zargin cewa tana kawo cikas ga tsarin jam’iyyun siyasa da dama, tana mai nuni da sabbin jam’iyyun siyasa da aka amince da su kwanan nan da suka hada da DLA da NDC da kuma NDP, wanda hakan ya kawo yawan jam’iyyun siyasa masu aiki zuwa 22, tare da jaddada cewa ita hukuma ce mai zaman kanta ba mai shiga siyasa ba.
Karanta: APC ta goyi bayan INEC kan soke amincewa da ADC, ta danganta hakan da hukuncin kotu
Game da shirin sabunta rajistar masu kada kuri’a a fadin kasa, INEC ta bayyana cewa shirin ya gabaci nadin Farfesa Amupitan, kuma tsari ne na gudanarwa kawai domin tantance sahihancin masu kada kuri’a, gyara rajista mai yawa da kuma cire sunayen wadanda suka rasu daga rijistar.
Ta ce wannan shiri zai gudana a dukkan kananan hukumomi da rumfunan zabe domin inganta sahihancin rajistar masu kada kuri’a, tare da tabbatar da cewa ba a ware wani yanki ko jam’iyya ko wani rukuni ba, kuma za a samar da hanyoyin zamani na digital ga masu kada kuri’a.
INEC ta jaddada cewa hankalinta na kan shirye-shiryen zabukan da ba na lokaci guda ba da za a yi a jihohin Ekiti da Osun, tare da gargadin ‘yan siyasa da su guji mayar da batutuwan gudanarwa na yau da kullum zuwa siyasa.
Hukumar ta kammala da cewa biyayyarta ga kundin tsarin mulki da muradin ‘yan Najeriya ne gaba daya, tana mai cewa kiraye-kirayen murabus din Farfesa Amupitan ba su da muhalli.
Wannan sanarwa na zuwa ne bayan jam’iyyar ADC ta bukaci shugaban INEC ya yi murabus nan take, tana zargin hukumar da nuna bangaranci da kuma tauye dimokuradiyyar Najeriya.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, shugaban ADC na kasa, David Mark, ya bayyana cewa jam’iyyar ta daina amincewa da hukumar zabe, yana mai zargin cewa matakan da INEC ta dauka sun saba doka da kuma ka’idojin dimokuradiyya, tare da cewa hukumar ta shiga rikicin cikin gida na jam’iyyar tare da yin watsi da hukuncin kotun daukaka kara.
Ya kuma zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da kokarin raunana jam’iyyun adawa kafin zaben 2027, yana mai cewa hakan wani bangare ne na shirin tabbatar da cewa jam’iyya mai mulki ta ci gaba da zama mafi karfi duk da matsalolin tsaro da tattalin arziki da ake fuskanta a kasar.












































