Wani daga cikin ministocin Tinubu ya yi murabus

Bola Tinubu Tinubu aaaaaaaaaaa 700x430

Ƙaramin Ministan kula da harkokin jin ƙai da rage talauci, Dakta Yusuf Tanko Sununu, ya yi murabus daga mukaminsa domin ci gaba da harkokin siyasa a jihar Kebbi, bisa umarnin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayar ga waɗanda ke son tsayawa takara a zaɓen 2027.

Sununu ya tabbatar da murabus ɗin nasa ga manema labarai a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne domin bin ƙa’idojin ƙasar da suka tanadi cewa duk mai rike da mukamin gwamnati da ke son tsayawa takara dole ne ya ajiye aiki.

Tsohon ɗan majalisar tarayya kuma likita wanda ya wakilci mazabar Shanga, Yauri da Ngaski, ana sa ran zai nemi kujerar sanata mai wakiltar Kebbi ta kudu a zaɓen 2027.

A baya, Sununu ya taɓa rike mukamin karamin ministan kula da ilimi kafin daga bisani a mayar da shi zuwa ma’aikatar harkokin jin ƙai da rage talauci.

Murabus ɗin nasa ya zo ne bayan wani minista, Yusuf Tuggar daga Bauchi, ya riga ya ajiye mukaminsa domin neman gwamna, lamarin da ke nuna yadda wasu manyan jami’an gwamnati ke ficewa domin neman mukaman zaɓe.

A halin yanzu, ranar ƙarshe da aka bai wa duk masu rike da mukaman gwamnati da ke son tsayawa takara su yi murabus ta cika, lamarin da ya haifar da ɗimbin hasashe da sa ido kan waɗanda za su sauka daga mukamansu kafin babban zaɓen shekarar 2027.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here