Gwamnatin tarayya ba ta bai wa ƙungiyoyin al’adu makamai don ayyukan tsaro a jihar Kwara ba – Ribadu

ribadu

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ayyukan yaki da ta’addanci da ake gudanarwa a wasu sassan jihar Kwara na gudana ne cikin tsari na doka da amincewar ƙasa baki ɗaya, tare da karyata rahotannin da ke nuni da cewa ana haɗa ƙungiyoyin al’adu a cikin ayyukan tsaron.

Shugaban sashen sadarwa na dabaru a cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa NCTC, Abu I. Micheal, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ofishin mashawarcin tsaro na ƙasa Malam Nuhu Ribadu ya fitar, domin mayar da martani ga rahotannin da ke yawo a wasu kafafen internet.

Sanarwar ta bayyana cewa NCTC, ƙarƙashin ofishin mashawarcin tsaron ƙasa, na da hurumin doka a ƙarƙashin dokar hana daƙile ta’addanci ta shekarar 2022, domin daidaitawa da tallafa wa dukkan hukumomin tsaro da na tattara bayanan sirri da ke aiwatar da ayyukan yaƙi da ta’addanci a faɗin ƙasar.

Ta ƙara da cewa wannan tsari na doka yana tabbatar da haɗin kai, bin doka da kuma aiwatar da ayyuka bisa amincewar ƙasa, tare da cewa dabarun yaƙi da ta’addanci na ƙasa na iya haɗa sojojin tsaro na yau da kullum da wasu ƙarin ma’aikata da aka tantance tare da horaswa ta musamman.

Sanarwar ta jaddada cewa duk irin waɗannan tura ma’aikata ana yin su ne ƙarƙashin cikakken iko da kulawar hukumomin tsaro da na bayanan sirri da aka amince da su, domin hana ƙungiyoyin ta’addanci da masu aikata laifuka samun mafaka a wurare masu wahalar shiga kamar dazuzzuka.

Karin labari: Wakilan tawagar Najeriya sun tabbatar da sakin jirgi da sojojin da aka tsare a Burkina Faso

Ta kuma bayyana cewa wannan tsarin aiki ba sabon abu ba ne, domin an taɓa amfani da shi a yankunan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, inda ya taimaka wajen inganta tsaro yadda ake iya gani.

Game da ayyukan da ake yi a jihar Kwara, sanarwar ta tabbatar da cewa ana gudanar da su ne cikin irin wannan tsari na doka da amincewar ƙasa, tare da nuna cewa rashin bayyana cikakkun bayanai ga jama’a da gangan ake yi saboda la’akari da tsaron ma’aikata, al’umma da ingancin ayyukan tsaro.

Gwamnatin tarayya ta kuma karyata ikirarin cewa tana haɗin gwiwa da wasu ƙungiyar al’adu wajen aiwatar da ayyukan tsaro masu amfani da ƙarfi, inda ta jaddada cewa ba ta ba da makamai, tallafi ko wata haɗin gwiwa ta hukuma da irin waɗannan ƙungiyoyi ba, kuma dukkan ƙarin ma’aikatan da ke shiga ayyukan tsaro ana ɗaukar su ne, ana horas da su kuma ana tura su ta hannun hukumomin tsaro da aka amince da su, bisa bin ka’idojin doka.

Sanarwar ta ƙare da kira ga jama’a da kafafen yaɗa labarai da su dogara da sahihan bayanai, su kuma rika neman bayani ta hanyoyin hukuma, tare da tabbatar da cewa cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa na ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da ƙarfafa tsaron ƙasa ta hanyar bin doka, ƙwarewa da haɗin kai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here