Shugaban hukumar kula da harkokin man fetur da ƙayyade farashi ta ƙasa NMDPRA ya musanta fitar da wata sanarwa dangane da zarge-zargen da shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya yi a kansa.
A cikin wata gajeriyar sanarwa da jaridar Solacebase ta samu, Ahmed ya ce bai ba da izinin fitar da sanarwar da ke yawo a kafafen sada zumunta ba, yana mai jaddada cewa ba daga gare shi ta fito ba kuma ba ta wakiltar matsayinsa.
Zargin ya samo asali ne bayan Dangote ya nemi a gudanar da cikakken bincike kan tushen kuɗin da Ahmed ya yi amfani da su wajen biyan kuɗin karatun ’ya’yansa a ƙasashen waje, tare da kira gare shi da ya bayyana kansa a gaban kotun ladabtarwa ta ma’aikatan gwamnati domin yin bayani ga jama’a.
Karin labari: ICPC ta tabbatar da karɓar ƙorafin Dangote kan shugaban hukumar NMDPRA, ta ce za a bincika ƙorafin yadda ya dace
Biyo bayan haka, Dangote ya miƙa ƙorafi ga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran laifuka masu alaƙa da shi ICPC, inda ya buƙaci a binciki harkokin kuɗin Ahmed, yana zargin cewa wasu ayyukansa na iya zama barazana ga tattalin arziki da amincewar masu zuba jari, musamman wajen ba da lasisin shigo da man fetur.
Sai dai Ahmed ya bayyana cewa duk da saninsa da zarge-zargen da ake yi a kansa da iyalinsa, ya zaɓi kada ya shiga muhawarar jama’a, yana mai cewa sanarwar da ake dangantawa da shi ba ta fito daga gare shi ba, kuma ba ya ɗaukar nauyin abin da ke cikinta.
Ya ƙara da cewa yana maraba da matakin da aka ɗauka na kai ƙorafin gaban hukumar ICPC, yana mai nuna cewa hakan zai ba da dama a binciki batun cikin adalci da kwanciyar hankali domin tsarkake sunansa.













































