Tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya soke shirin kafa wata ƙungiyar Hisbah mai zaman kanta da aka sanya wa suna Hisbah Fisabilillahi a jihar Kano.
Sanarwar soke shirin ta cikin wata sanarwa da babban daraktan Cibiyar Ƙara Ingancin Aiki ta Ƙasa kuma jigo a jam’iyyar APC a Kano, Baffa Babba Dan Agundi, ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa an yanke matakin ne bayan tattaunawa mai zurfi.
Sanarwar ta nuna cewa an cimma matsayar ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da ya haɗa wakilai daga ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano, wanda aka gudanar a ofishin kamfen na Tinubu a jihar.
Ta bayyana cewa matakin janyewa daga shirin ya biyo bayan ra’ayoyi da damuwa masu yawa da jama’a suka nuna game da shirin kafa ƙungiyar Hisbah mai zaman kanta a jihar.
Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa manyan masu ruwa da tsaki sun shiga tsakani domin hana rikici da kare zaman lafiya da kwanciyar hankali, ciki har da gwamnatin jihar Kano, Hukumar Tsaro ta DSS da kuma Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Haka kuma an yanke shawarar dakatar da shirin ne domin bai wa gwamnatin jihar Kano damar duba batun sallamar wasu jami’an Hisbah tare da magance matsalar ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna.
Sanarwar ta jaddada girmamawa ga Hukumar Hisbah da aka kafa bisa doka a jihar Kano, tare da bayyana aniyar ci gaba da goyon bayan hukumomin tsaro na halal domin tabbatar da doka da oda da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar Kano da ƙasar baki ɗaya.













































