Tsohon babban mai shari’ar Najeriya Tanko Muhammad ya rasu

Tanko Muhammad

Tsohon babban mai shari’ar Najeriya Alkali Ibrahim Tanko Muhammad mai ritaya ya rasu.

Rahotanni sun nuna cewa ya rasu ne da safiyar Talata a wani asibiti da ke ƙasar Saudiyya bayan rashin lafiya.

Mutuwarsa ta samu tabbaci ne ta cikin sanarwar ta’aziyya da ƙungiyar ɗaliban shari’ar Musulmi ta Najeriya ta fitar daga hedikwatarta ta ƙasa da ke Abuja.

Ƙungiyar ta bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya.

Ƙungiyar ta bayyana cewa rasuwar tsohon babban mai shari’ar ta yi matuƙar girgiza bangaren shari’a na Najeriya, sana’ar lauya da kuma al’ummar Musulmi, tana mai nuni da irin rawar da ya taka a harkokin shari’a da rayuwar jama’a.

Sanarwar ta ƙara da cewa a tsawon aikinsa a bangaren shari’a, Alkalin Tanko Muhammad ya kasance abin koyi wajen adalci, jarumtaka da bin doka, tare da tafiyar da ayyukansa cikin hikima da nutsuwa a lokacin da yake rike da mukamin babban mai shari’ar Najeriya.

Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa marigayi Alkalin ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen tarbiyya da jagoranci, musamman ga matasa ɗaliban shari’a Musulmi a faɗin ƙasar, inda ya kasance kamar uba da ginshikin ƙarfafawa a gare su.

Sanarwar ta miƙa ta’aziyya ga iyalansa, bangaren shari’ar Najeriya da al’ummar ƙasar gaba ɗaya, tare da yin addu’ar Allah ya gafarta masa kura-kuransa, ya karɓi ayyukansa na alheri, ya kuma sanya shi cikin mafi girman matsayi a Aljannar Firdausi.

Marigayi Ibrahim Tanko Muhammad ya yi wa bangaren shari’ar Najeriya hidima tsawon shekaru masu yawa, inda ya kai kololuwar mukami a fannin shari’a, ya bar tarihin aiki da ya yi tasiri a muhimman lokuta na tarihin shari’ar ƙasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here