Kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar wakilai kan albarkatun man fetur ya gayyaci matatar Dangote da Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur da ƙayyade farashi ta ta ƙasa NMDPRA domin warware sabanin da ke barazana ga sashen rarraba man fetur a ƙasa.
Shugaban kwamitin, Ikenga Ugochinyere, ya bayyana hakan, bayan taron gaggawa da aka gudanar a Abuja cewa tashin hankalin da ke ƙaruwa na iya lalata daidaiton da aka samu kwanan nan a fannin man fetur.
Ya ce dole ne kwamitin ya ɗauki mataki cikin gaggawa, ganin yadda ake ci gaba da ƙoƙarin daidaita samarwa, farashi da kuma tsarin kula da harkokin man fetur a sabon yanayin bayan cire tallafin man fetur a Najeriya.
Labari mai alaƙa: Dangote ya zargi shugaban hukumar NMDPRA da kashe Dala Miliyan 5 wajen biyan kudin karatun ’ya’yansa a kasashen waje, ya bukaci a yi bincike
Muhimmin abin da ke haifar da sabon rikici shi ne damuwa da zarge-zargen da Alhaji Aliko Dangote ya yi kan NMDPRA, lamarin da ya tayar da rikici a sashen rarraba man fetur na ƙasa.
Ugochinyere ya bayyana cewa kwamitin na ƙoƙarin kare daidaiton da aka samu da ƙyar, inda ya jaddada cewa samun mafita mai ɗorewa na buƙatar gano muhimman matsaloli, wanda hakan ya sa aka gayyaci shugabannin matatar Dangote da NMDPRA.
Ya ƙara da cewa ƙorafe-ƙorafen da aka karɓa sun shafi bayar da lasisin shigo da mai da kuma ko matatun man fetur na cikin gida na iya biyan buƙatar man fetur ta yau da kullum a Najeriya.
Kwamitin, ya tabbatar da cewa za a duba dukkan batutuwan da suka rage lokacin da masu ruwa da tsaki a fannin tace man fetur da hukumomin kula da harkoki suka bayyana a gaban kwamitin.
NAN.












































