Gwamnatin tarayya ta sanar da haramcin karɓar sabbin ɗalibai da kuma sauyawa ɗalibai zuwa ajin babban sakandare na uku SS3 a dukkan makarantu na gwamnati da masu zaman kansu a faɗin ƙasar nan.
Matakin ya zo ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin da ake yi na dakile satar jarrabawa da kuma rage yawaitar matsalolin da ke tattare da jarrabawar kammala sakandare, musamman amfani da abin da ake kira cibiyoyi na musamman a lokacin jarrabawar, lamarin da ke lalata mutunci da sahihancin tsarin ilimi a Najeriya.
Ma’aikatar ilimi ta tarayya ta bayyana cewa wannan sabon tsari zai fara aiki daga shekarar karatu ta 2026 zuwa 2027, tare da jaddada cewa za a yi aiki da shi a dukkan makarantu ba tare da bambanci ba.
Hakan na cikin wata sanarwa da daraktar yaɗa labarai da hulɗa da jama’a ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ta sanya hannu.
Karanta: Gwamnatin tarayya ta kafa cibiyoyin koyarwa 119 domin inganta ilimin Almajirai
A karkashin wannan tsari, za a ci gaba da ba da damar karɓa da sauyawa ɗalibai aji ne kawai zuwa SS1 da SS2, yayin da karɓa ko sauyawa ɗalibai zuwa SS3 ba za a amince da shi ba a kowane hali.
Ma’aikatar ta fayyace cewa manufar wannan mataki ita ce hana sauya ɗalibai a ƙarshen lokaci zuwa makarantu da ake ganin suna ba da wata fa’ida ta musamman a jarrabawa, al’adar da ke ƙara ƙarfafa satar jarrabawa, tare da tabbatar da cikakken sa ido na ilimi da ci gaba da daidaito a koyarwa da koyo.
Gwamnatin tarayya ta umarci masu makarantu, shugabannin makarantu da masu kula da harkokin ilimi a duk faɗin ƙasar nan da su bi wannan umarni yadda ya kamata.
Sanarwar ta gargaɗi cewa duk wanda ya saɓa zai fuskanci hukunci bisa ga dokoki da ƙa’idojin ilimi da ake da su, a wani yunkuri na kare ƙa’idodin ilimi da dawo da amincewar jama’a kan jarrabawa a Najeriya.













































