NELFUND za ta faɗaɗa shirin bada lamuni zuwa horon sana’o’i

NELFUND 750x430

Asusun bada lamunin ilimi na ƙasa NELFUND ya bayyana shirin faɗaɗa tsarin bayar da lamunin ɗalibai domin ya haɗawa da shirye-shiryen horon sana’o’i da bunƙasa ƙwarewar aiki a faɗin ƙasa.

Manajan Darakta na asusun, Akintunde Sawyerr, ya ce matakin ya dace da manufar gwamantin tarayya wajen haɓaka ilimi da ƙwarewar fasaha, tare da mai da hankali kan tsarin da ya wuce karatun jami’a kaɗai.

Ya bayyana cewa shirin yana nuna aniyar shugaban ƙasa Bola Tinubu wajen bunƙasa ci gaban ɗan adam cikin tsarin da ya haɗa dukkan sassa na ilimi da fasaha domin ƙara samar da damar shiga fannin aiki.

Sawyerr ya ce duk da cewa NELFUND tun farko yana tallafa wa ɗaliban manyan makarantu, yanzu ana shirye-shiryen faɗaɗa hakan domin bai wa masu ilimin sana’o’i da fasahar aiki damar samun lamuni a dukkan sassan ƙasa.

Ya ce matakin ci gaban ƙasar na gaba yana buƙatar daidaito tsakanin ilimi da fasahar hannu, inda ma’aikatu da dama ciki har da ma’aikatar raya matasa, ma’aikatar ilimi da ma’aikatar tattalin arzikin zamani suke da alhakin aiwatar da shirye-shiryen ƙwarewar aiki.

Ya kara da cewa ƙasar na bukatar matakin da ya haɗa tsara aiki, gina abin da aka tsara da kuma gudanar da shi, tare da samar da ƙwararru da zasu iya aiwatar da ayyukan fasaha ba tare da dogaro ga bayanin rubutu kaɗai ba.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa NELFUND yana ƙara inganta shirye-shiryen da za su bai wa horon sana’o’i matsayi mai muhimmanci a tsarin lamuni domin ciyar da ƙasar gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here