Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da sauye-sauye a cikin ma’aikatanta, domin kawar da maimaituwar aiki tare da inganta yadda ake gudanar da ayyuka.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Darakta, kuma Jami’ar Yaɗa Labarai na hukumar, Hajiya Fatima Usara, ta fitar a Abuja ranar Juma’a.
Ta bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan shawarar da Kwamitin gudanarwa na hukumar ya cimma a zama na 14 da aka yi tsakanin 26 zuwa 27 ga watan Agusta, 2025.
A cewar ta, manufar matakin ita ce inganta tsarin aiki da ƙarfafa ma’aikata domin samun ƙarin kwazo da jajircewa.
Labari mai alaƙa: Hajjin 2026: Kano ta sanya Naira Miliyan 8.5m a matsayin kuɗin ajiya, daidai lokacin da NAHCON ta baiwa jihar kujeru 5,684
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Usman, ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da ɗaukar matakai na ƙarfafa ma’aikata tare da tabbatar da cika nauyin da aka dora mata wajen kula da alhazai na Najeriya.
Haka kuma, NAHCON ta ce za ta ci gaba da ƙaddamar da wasu sauye-sauye da nufin ƙara yawan aiki da inganci.













































