Kano: Kotu ta kori dan majalisar tarayya na NNPP kan amfani takardar makaranta ta jabu

election tribunal 750x430
election tribunal 750x430

Kotun sauraren kararrakin zabe ta Majalisar Dokoki ta kasa da ta Jiha ta tabbatar da cewa Idris Dankawu na jam’iyyar NNPP ya yi jabun takardar shaidar kammala karatu a ta  WAEC, da ya gabatar da shi domin tsayawa takarar kujerar dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Kumbotso.

Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa Munir Babba Danagudi ya shigar da karar ne yana addu’a ga kotu da ta bayyana cewa Dankawu ya yi jabun satifiket dinsa na Sakandare domin samun gurbin shiga makarantar Nuhu Bamalli Polytechnic Kaduna.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here