Gwamnan jihar Nasarawa Alhaji Abdullahi Sule ya dage bikin kaddamar da majalisar dokokin jihar Nasarawa karo na 7.
A cikin wata sanarwar da mukaddashin magatakardar majalisar, Ibrahim Musa ya fitar, ya ce an dage zaman ne bisa shawarar tsaro.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Mukaddashin magatakardar Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Ibrahim Musa, yana so ya sanar da dukkan zababbun ‘yan majalisar da sauran jama’a cewa, bisa la’akari da shawarwarin tsaro, an shirya kaddamar da zaman farko na majalisar ta 7, kamar yadda sanarwar ta bayyana. Mai Girma Gwamnan Jihar Nasarawa Engr. Abdullahi Sule, ya dage shi.”
Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa za a sanar da sabon rana da lokaci ga zababbun mambobin da sauran jama’a.
Daga karshe sanarwar ta bayyana nadama kan duk wata matsala da dage lolacin ta haifar.













































