Masari Ya Kai Ziyarar Bankwana Ga Sarakuna, Tareda Neman Hadin Kan su.

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya kai ziyarar ban kwana ga mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir-Usman da na Daura, Alhaji Umar Faruq-Umar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya rawaito cewa gwamnan ya ziyarci Masarautar Katsina ne a ranar laraba inda kuma ya je Daura a ranar Alhamis a wani bangare na kawo karshen wa’adinsa a ranar 29 ga watan Mayu.

Da yake jawabi a Daura, Masari ya ce gwamnatinsa ta yi duk mai yiwuwa wajen shigar da sarakunan addini da na gargajiya wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a jihar.

A cewarsa, ziyarar ta bankwana ce domin neman karin hadin kai a tsakanin al’ummar Katsina, ba tare da la’akari da shiyyoyin su, kananan hukumomi ko al’ummominsu ba.

Ya ce mutanen Katsina tsintsiya ce guda, ya kuma roke su da su ci gaba da zaman hadin kai, kamar yadda marigayi Sardaunan Sakkwato, Sir Ahmadu Bello ya yi.

“Ziyarar da muka kai kan masarautun wani yunƙuri ne don nuna godiya da goyon bayan da suka bayar don samun nasarar mulkina na shekaru takwas,” in ji Masari.

Gwamnan mai barin gado ya bayyana cewa kyakkyawar alakarsa da masarautun biyu za ta ci gaba da kasancewa ko da bayan wa’adinsa.

A nasu jawabin, sarakunan biyu sun yaba wa gwamnan bisa jajircewarsa da kokarin su na kawo ci gaban jihar.

Mai martaba Sarkin Katsina wanda ya yabawa gwamnan bisa salon shugabancinsa, ya ce abin da ya dace a yi koyi da shi, ya kuma gode masa bisa goyon bayan da yake baiwa masarautar.

Anasa bangaren Sarkin Daura ya ce ba zasu taba mantawa da Masari ba saboda goyon baya da jajircewarsa wajen ci gaban masarautun Katsina baki daya. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here