Mahukuntan ƙasar Saudiyya sun bayyana cikakkun ƙa’idoji da sharuddan lafiya ga duk masu niyyar gudanar da aikin Hajji na shekarar 2026, wanda ya yi daidai da shekarar 1447 bayan hijira.
Wannan sanarwa ta fito ne daga ma’aikatar lafiya ta Saudiyya, inda ta jaddada muhimmancin tabbatar da cewa kowace ƙasa, ciki har da Najeriya, ta tabbatar da lafiyar alhazanta kafin tafiya.
A cewar ƙa’idojin, ana buƙatar maniyyata su gabatar da takardar shaidar lafiya daga ƙasashensu, wadda za ta tabbatar cewa ba su da wata cuta mai tsanani da za ta iya kawo barazana ga lafiyarsu ko ta wasu.
Cutar da za ta iya hana mutum tafiya ta haɗa da matsananciyar cutar zuciya, huhu, koda, ko hanta, da kuma cututtukan kwakwalwa da ke hana tunani ko motsi yadda ya kamata.
Haka kuma mata masu juna biyu da ke da haɗari da masu jinya na cutar daji a ƙarƙashin magani na musamman suna cikin waɗanda ba za su samu damar tafiya ba.
Ƙasar Saudiyya ta kuma bayyana cewa dole ne kowanne alhaji ya gabatar da shaidar allurar rigakafi daga ƙasarsa, wadda ke tabbatar da cewa an yi masa allurar kariya daga muhimman cututtuka kafin shiga ƙasar.
Wannan ya zama muhimmin ɓangare na tsarin kula da lafiyar masu aikin hajji domin kare su da sauran mahajjata daga yaduwar cututtuka.
Hukumomin lafiya za su gudanar da binciken lafiya a dukkan hanyoyin shiga ƙasar Saudiyya.
Duk wanda bai cika sharuddan ba ana iya ƙin shigar da shi, killace shi, ko kuma yi masa ƙarin bincike na likitanci.
Haka kuma Saudiyya ta bayyana cewa tana da ikon ƙara wasu matakan kariya idan aka sami barkewar wata cuta ta duniya ko matsalar lafiya ta gaggawa a matakin ƙasa da ƙasa tare da haɗin gwiwar hukumar lafiya ta duniya.
Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta shawarci duk maniyyata su fara shirin cika waɗannan buƙatu na lafiya tun da wuri, ciki har da yin allurai da kuma gwaje-gwajen lafiya kafin lokacin tafiya.
Haka kuma hukumar tare da kwamitocin jin dadin alhazai na jihohi da kamfanonin yawon bude ido masu lasisi za su haɗa kai domin tabbatar da bin ƙa’idojin, don guje wa tsaiko ko jinkiri lokacin isa ƙasar Saudiyya domin aikin Hajjina 2026.













































