Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya jagoranci taron kaddamar da wata sabuwar kungiyar siyasa mai suna The National Movement TNM, wadda zata kunshi wasu manyan siyasar kasar nan.
Cikin fitattun ƴan siyasa da suka halarci taron sun haɗa da Alhaji Tanko Yakasai da Capt Idris Wada, tsohon gwamnan Kogi da Rufai Alkali da Aminu Ibrahim Ringim, tsohon dan takarar gwamna a jihar Jigawa da kuma Inijiniya Buba Galadima.
An gudanar da taro ne a International Conference Centre da ke Abuja, babban birnin tarayyar kasar.
A jawabin Kwankwaso, ya ce wasu ƴan Najeriya ne da suka damu da abin da ke faruwar a ƙasar suka haɗa kai don ceto ta daga mawuyacin halin da ta shiga.
Ya ce yunƙuri ne na ƴan Najeriya masu kishi da suke zaune a gida da kasashen waje.
Rabi’u Musa Kwankwaso: Tsohon gwamnan Kano ya ce bai yi mamakin rikicin APC a Kano ba
Kwankwaso ya yi wa Buhari wasika kan mace-macen Kano
A cewar Kwankwaso za su duƙufa wajen farfaɗo da tattalin arzikin kasar da inganta rayuwar ƴan kasa a birni da karkara
Ya ce sun shirya tsaf domin tunkarar matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.
Kwankwaso ya ce za su yi wa makiyaya gata na ganin cewa ba a cinye musu burtalai ba, sannan za su bai wa manoma dukkan kariyar da suke bukata.
Tsohon gwamnan na jihar Kano, wanda dan jam’iyyar PDP ne, bai bayyana mukamin da yake son nema ba a wannan sabuwar kungiya ta siyasa.
Sai dai ana rade radin cewa zai fita daga jam’iyyar PDP sakamakon rashin jin dadin abubuwan da ke faruwa a cikinta. Kodayake bai tabbatar da hakan ba.













































