Ɗalibai sun baje kolin basirarsu yayin da Kano ta gudanar da bikin ranar Kimiyya ta Duniya a 2025

WhatsApp Image 2025 11 17 at 22.09.59 750x430

Jihar Kano ta ƙaddamar da bikin makon kimiyya na 2025 a wani ɓangare na ranar Kimiyya ta Duniya, inda ɗalibai, masu kirkire-kirkire da manyan baƙi suka hadu domin nazarin ci gaba da damar da ke cikin kimiyya da fasaha.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa bikin zai gudana na kwanaki uku daga Litinin 17 zuwa Laraba 19 ga Nuwamba a cibiyar fasahar zamani ta Ma’aikatar Kimiyya, Fasaha da Kirkire-kirkire, ƙarƙashin taken “Amincewa, Sauyi da Gobe: Kimiyyar da muke buƙata zuwa shekara 2050.”

A cikin taron an shirya laccoci, gabatar da takardu, wasannin gasa, muhawara da nune-nunen kirkire-kirkire daga makarantu, jami’o’i da masu kirkire-kirkire masu zaman kansu.

Ma’aikatar Kimiyya, Fasaha da Kirkire-kirkire ce ke tsara wannan taro duk shekara domin yaɗa ilimin kimiyya da fasaha, karfafa matasa su rungumi waɗannan fannonin, da kuma samar da damar hada kai da masana’antu da kasuwanci.

Kwamishinan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-kirkire, Dr. Yusuf Ibrahim Kofarmata, ya bayyana jin daɗinsa kan yawan mahalarta taron, yana karfafa ɗalibai su rungumi ilimi musamman a fannin kimiyya da fasaha, tare da bayyana cewa za a bai wa masu nasara kyaututtuka domin tallafa wa ayyukansu.

Injiniya Aminu Shehu Danhassan, Daraktan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-kirkire na ma’aikatar, ya ce wannan biki na ba da dama ga ɗalibai da masu kirkire-kirkire su nuna basirarsu, su tallata kayayyakin kirkirarsu, da haɗa kai da masu saka jari da masana’antu.

A nasu ɓangaren, ɗalibai sun shiga gasa da nune-nune, suna gabatar da ayyuka daga na’urorin fasaha zuwa gwaje-gwajen kimiyya, inda suka nuna ƙirƙira, iya warware matsaloli, da fahimtar ka’idojin kimiyya a aikace.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here