Rundunar ‘yan sanda ta jihar Akwa Ibom ta bayyana dagacin kauyen Ine Eyoabasi Fishing Village a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin shiga cikin wata kungiyar ‘yan ta’adda da masu fashin teku da ke aiki a yankunan gabar ruwa na jihar.
Kwamishinan ‘yan sanda CP Baba Mohammed Azare ne ya sanar da hakan a lokacin taron manema labarai da aka gudanar a Uyo, inda ya bayyana cewa rundunar tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Marine Hunters sun cafke wani mutum mai suna Samuel Geofrey, wanda ya bayyana cewa bindigarsa tana hannun dagacin kauyen.
A cewar rundunar, lokacin da jami’an yan sanda suka isa kauyen domin gudanar da bincike, dagacin ya tsere, sai dai binciken da aka yi a gidansa ya kai ga gano kayayyaki da ake zargin an sace daga masu zirga-zirga ta ruwa, ciki har da injinan jirgin ruwa, janareto, injin dinki da wasu kayan amfanin gida.
Kwamishinan ya bayyana cewa ana ci gaba da neman dagacin da ya tsere tare da tabbatar da cewa duk wanda ke da hannu a laifi ba zai tsira daga hukunci ba.
Ya ƙara da cewa an kama wasu da ke amfani da kayan raye-raye wajen aikata fashi da kuma shugabannin ƙungiyar “Ekpo masquerade” bisa zargin toshe hanya da karɓar kuɗin haram.
Rundunar ta kuma lalata wata haramtacciyar masana’antar ƙera bindigogi a garin Ekiti Itam, inda aka kama mutane biyu tare da kayan ƙera makamai.
Kwamishinan ya yaba wa jami’an ‘yan sanda bisa jajircewa da kuma gode wa jama’a bisa haɗin kai, yana mai tabbatar da cewa Akwa Ibom za ta ci gaba da kasancewa cikin jihhohin da suka fi aminci a Najeriya.













































