Ƙungiyar likitoci ta NARD ta tsunduma yajin aiki na sai Baba ta gani

Doctors NARD 750x430

Ƙungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya NARD, ta fara yajin aiki na sai Baba ta gani daga yau, 7 ga Afrilu, matakin da ke barazanar jefa asibitocin gwamnati cikin tsaiko a faɗin ƙasa.

Yajin aikin ya biyo bayan zargin da likitocin ke yi na cewa gwamnatin tarayya ta dakatar da aiwatar da sabon tsarin biyan alawus-alawus, wanda ke cikin yarjejeniyar da aka cimma bayan yajin aikin shekarar 2025.

Ƙungiyar ta bayyana matakin na gwamnati a matsayin abin takaici, ta na mai cewa hakan ne ya tilasta musu ɗaukar wannan mataki, duk da cewa ana iya kauce masa.

NARD ta ce, Majalisar zartarwarta ta ƙasa ta amince da shiga “cikakken yajin aiki” bayan nazari kan sauye-sauyen manufofin gwamnati da kuma gazawar cika alkawurra.

Daga cikin buƙatun da likitocin ke gabatarwa akwai dawo da tsarin alawus din da aka dakatar, biyan bashin karin girma da albashi, biyan bashin alawus na watanni 19, da kuma sakin kuɗaɗen horar da likitoci na shekarar nan da muke ciki ta 2026.

Tun bayan hawan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, likitocin sun shafe akalla kwanaki 51 suna yajin aiki a lokuta daban-daban, lamarin da ke ƙara jefa shakku kan dorewar yarjejeniyar gwamnati da ma’aikatan lafiya a faɗin Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here