Asusun bada Lamunin karatu ga ɗalibai a ƙasar nan (NELFUND) ya sanar da buɗe shafinsa na Internet domin karɓar buƙatun lamuni daga dalibai na manyan makarantu a fadin ƙasar domin zango na karatu na shekarar 2025/2026.
Asusun ya bayyana cewa za a fara karɓar buƙatun ɗaliban daga ranar Alhamis 23 ga Oktoba, 2025, kuma za a rufe daga ranar Asabar 31 ga Janairu, 2026.
Wannan na ƙunshe ne a cikin sanarwar da daraktan sashen sadarwa da dabaru na asusun, Oseyemi Oluwatuyi, ya fitar a ranar Talata, inda ya bukaci daliban da suka cancanta su yi amfani da wannan dama don neman tallafin kuɗin karatu.
NELFUND ya shawarci sabbin daliban da suka samu gurbin karatu da su yi amfani da lambar shigar su ta JAMB ko lambar shiga makaranta a maimakon lambar rajista, domin sauƙaƙa tsarin neman lamuni cikin sauƙi.
Haka kuma, asusun ya roƙi jami’o’i da sauran manyan makarantu da su nuna fahimta kan batun lokacin rajista da biyan kudin makaranta ga daliban da ake ci gaba da tantance buƙatun lamuninsu, don kauce wa matsaloli.
Ya ƙara da cewa duk wata cibiya da ba ta fara sabon zangon karatunta ba ta tura wasiƙa ga asusun NELFUND tare da jadawalin karatunta na shekara domin samun daidaiton tsari.
Asusun ya tabbatar da cewa yana da cikakken shiri na tabbatar da cewa babu wani ɗalibin Najeriya da zai rasa damar yin karatun jami’a, kwaleji ko makarantar kimiyya saboda ƙarancin kuɗi.
Asusun Lamunin Dalibai na Najeriya (NELFUND) an kafa shi ne domin samar da lamunin karatu ba tare da ruwa ba ga daliban manyan makarantu, bisa manufar shugaban ƙasa Bola Tinubu na faɗaɗa damar samun ilimi da rage ƙalubalen kuɗi ga matasa a fadin ƙasar.













































