Zaben kenya: Kotun koli ta tabbatar da nasarar William Ruto

download
download

Kotun kolin Kenya ta tabbatar da William Ruto a matsayin zababben shugaban kasar, a yayin da ta yi watsi da karar da da aka shigar gabanta ana neman ta tsoke zaben shugaban kasar.

Abokin karawar tasa a zaben Raila Odinga, tare da wasu mutane ne suka shigar da karar, inda suke zargin tafka magudi a zaben da aka gudanar ranar 9 ga watan Agusta.

Mista Ruto ya yi nasara da kashi 50.5 cikin dari na kuri’un da aka kada.

A mako mai zuwa ne dai za a rantsar da mista Ruto mai shekara 55, a matsayin shugaban kasar na biyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here