Yanzu-yanzu: Gwamnan Bayelsa ya koma jam’iyyar APC

WhatsApp Image 2025 11 03 at 15.26.58

Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranci manyan jiga-jigan jam’iyyar APC zuwa Yenagoa domin taron maraba da gwamnan.

Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, mataimakinsa Barau Jibrin, da gwamnonin Ogun, Ondo, Delta da Akwa Ibom Dapo Abiodun, Lucky Aiyedatiwa, Sheriff Oborevwori da Umo Eno duk sun halarci bikin.

Masu goyon bayan jam’iyyar APC sun cika wajen taron suna daga tutoci da rera waƙoƙin maraba da shigowar Diri cikin jam’iyyar.

Wannan sauyin siyasa na ɗaya daga cikin manyan canje-canjen da suka faru a jihar Bayelsa, wadda aka dade ana ɗauka a matsayin sansanin jam’iyyar PDP.

A bana kawai, PDP ta rasa gwamnoni hudu da suka hada da Oborevwori, Eno, Diri da kuma gwamnan Enugu, Peter Mbah.

Sauyin sheka da Diri ya yi na zuwa ne yayin da ake ci gaba da ganin fitattun ‘yan siyasa suna komawa APC gabanin zaɓen shekarar 2027.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here