Yanzu-yanzu: Ƴan wasan Super Eagles sun yi barazanar ƙin buga wasa da Aljeriya

Super Eagles1

Ƴan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasa Super Eagles sun yi barazanar ƙin tafiya birnin Marrakesh domin buga wasansu na gaba a gasar kofin nahiyar Afirka, matuƙar Hukumar Kwallon Ƙafa ta Najeriya ba ta biya dukkan alawus-alawus da kuɗaɗen ladan nasarori da suke bin su ba.

Wata majiya mai tushe daga cikin tawagar ne ya sanar da jaridar Vanguard haka.

Ya kuma bayyana cewa har yanzu ƴan wasa da jami’ai na jiran a biya su kuɗaɗen ladan nasarorin da suka samu tun daga farkon gasar, lamarin da ke haddasa rashin jin daɗi a cikin tawagar.

Bayanan sun nuna cewa har yanzu ba a biya kuɗaɗen ladan nasara na wasanni huɗu da aka buga da ƙungiyoyin Tanzaniya, Tunisiya, Yuganda da Mozambik ba, duk da cewa an riga an kammala waɗannan wasanni.

Duk da jajircewar da tawagar ke nunawa wajen ci gaba da fafatawa a gasar, sun jaddada cewa ba za su yi atisaye ko tafiya Marrakesh domin wasan da Aljeriya ba, sai an warware batun kuɗaɗen da ake bin su.

Idan za a iya tunawa, a watan Nuwamba da ya gabata, ƴan wasan Super Eagles sun taɓa yin irin wannan barazana ta ƙin buga wasan neman tikitin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 da Gabon, sakamakon rashin biyan wasu hakkokinsu.

A wancan lokaci, ƴan wasa da ma’aikatan tawagar sun bayyana rashin fitarsu atisaye a Moroko saboda matsalolin kuɗaɗen da ba a biya ba, inda suka nuna cewa suna jiran warware matsalar cikin gaggawa domin ci gaba da shirin wasannin da ke gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here