Yan sandan kasa da kasa na ‘interpol’ na neman wasu ‘yan Nijeriya ruwa a jallo sakamakon zarginsu da safarar mutane da ƙwayoyi

1735122212605

Kimanin ‘yan Najeriya 14 ne rundunar ‘yan sandan kasa da kasa ta bayyana cewa tana nemansu bisa laifukan da suka hada da safarar mutane, safarar miyagun kwayoyi, fashi, damfara da jabu da dai sauransu.

An tattaro a ranar Talata daga Red Notices da aka buga a shafin INTERPOL cewa ‘yan Najeriya 14 na neman kasashe daban-daban inda ake zarginsu da aikata laifin.

Sanarwar ta bayyana wadanda ake nema ruwa a jallo da Felix Omoregie, Jessica Edosomwan, Uche Egbue, Jude Uzoma, Chinedu Ezeunara, Benedict Okoro, Ikechukwu Obidiozor, da Alachi Stanley.
Sauran sun hada da Bouhari Salif, Timloh Nkem, Austine Costa, Okromi Festus, Akachi Vitus da Mary Eze.

A cewar sanarwar, Omoregie na neman hukumar kasar Belgium bisa zarginsa da jagorantar wata kungiyar masu aikata laifuka da ke cin zarafin kananan yara domin yin karuwanci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here