Yan sanda sun kama Kansila mai ci yana taimakawa masu garkuwa a Kaduna

'Yan sanda sun kama wata mata da ake zargin ta kashe mijinta, ta jefar da gawar a wani kango
'Yan sanda sun kama wata mata da ake zargin ta kashe mijinta, ta jefar da gawar a wani kango

Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta cafke wani Kansila mai ci dauke da bindiga kirar AK47 a yankin Galadimawa dake karamar hukumar Giwa.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna ASP Muhammed Jalige, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a aka rabawa manema labarai a Kaduna.

Yace jami’an tawagar Puff adder ne suka yi nasarar kama wanda ake zargin, a yayin da suka hange shi dauke da buhu a gaban mashin a hanyar shiga garin Galadimawa dake karamar hukumar Giwa, wanda hakan yasa jami’an suka zarge shi.

Bayan dakatar da shi ne suka bincika buhun, a yayin binciken ne suka samu bindiga kirar AK47 da alburusai a cikin ta, daga nan ne suka kama shi.

An gano Kansilan mai suna Abdulrahman Adamu, cewa daya ne daga cikin yan majalisar karamar hukumar Soba dake jihar Kaduna dake wakiltar mazabar Kinkiba, ya kuma bayyana cewa ya samu bindigar ne a hannun abokan aikinsa zai kuma mikawa yan bindiga dake yankin Galadimawa, a cewar ASP Muhammed Jalige.

Kwamishinan Yan sandan jihar Kaduna Yekini Adiyo Ayoku, ya bukaci jami’an tsaro da su tabbatar sun zurfafa bincike akan lamarin don kama duk wani mai hannu a ciki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here