Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne su uku da DPO sun mutu yayin musayar wuta a Katsina

police

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar wasu ‘yan bindiga uku da kuma Baturen ƴan sanda na karamar hukumar Rimi, CSP Muhammad Sani-Kabir, yayin musayar wuta ranar Juma’a.

Sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Aliyu Abubakar, ya fitar a Katsina ta bayyana haka.

Ya ce ranar 13 ga Fabrairu, 2026, da misalin karfe 2:00 na rana, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne dauke da muggan makamai sun kai hari kauyen Magaje da ke karamar hukumar Rimi, inda suka kwashe dabbobi tare da tserewa kafin isowar jami’an ‘yan sanda.

Bayan samun rahoton, DPO na Rimi tare da hadin gwiwar ofisoshin makwabta da sojoji suka tattara jami’ai suka nufi wurin.

Tawagar ta bi sawun wadanda ake zargi tare da tare su a kauyen Magaje, inda aka yi musayar wuta.

Jami’an tsaron sun kwato dukkan dabbobin da aka kwashe tare da kashe ‘yan bindiga uku.

Sai dai DPO ya samu mummunan harbi daga ‘yan bindigar wanda ya yi sanadin mutuwarsa, yayin da wani dan sanda ya ji rauni a hannunsa.

An garzaya da dan sandan da ya ji rauni asibiti domin kula da lafiyarsa, kuma yana amsa magani.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Katsina, Bello Shehu, ya yaba da jarumtaka da hadin kan jami’an tsaron suka nuna, tare da yin Allah-wadai da lamarin.

Ya kuma yi alhinin rasuwar jami’in, yana mai bayyana shi a matsayin kwararren dan sanda mai gaskiya da kwarewa, tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalansa da abokansa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here