Tura sojoji aikin tsaron cikin gida na raunana ƴan sanda – Tsohon Babban Hafsan sojojin ƙasa 

army 750x430

Tsohon Babban Hafsan Sojojin ƙasa, Laftanar Janar Tukur Buratai mai ritaya, ya yi gargadin cewa yawaitar tura sojoji domin ayyukan tsaron cikin gida a fadin Najeriya na rage karfin rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro na farar hula, duk da cewa hakan na iya samar da kwanciyar hankali na dan lokaci.

A halin yanzu ana tura jami’an sojoji zuwa sassa daban-daban na kasar nan, ciki har da Babban Birnin Tarayya, domin tallafa wa ayyukan tsaron cikin gida.

Buratai ya bayyana hakan ne yayin gabatar da jawabin bude taro a bikin tunawa da ranar sojojin kasa na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja.

Ya bayyana cewa yaduwar kasancewar sojoji a dukkan jihohi 36 na Najeriya na rage ci gaba da ingancin aikin ‘yan sanda da hukumomin leken asiri na cikin gida, wadanda ya kamata su kasance a sahun gaba wajen kula da tsaron cikin gida.

Ya yi nuni da cewa wannan yanayi na haifar da dogaro da sojoji fiye da kima, yana raunana karfin ‘yan sanda tare da matsa wa albarkatun tsaro.

Karanta: Masu ruwa da tsaki a bangaren shari’a sun dauki mataki don daƙile cin zarafin umarnin kotu da tsare mutane ba bisa ka’ida ba a Kano

A cewarsa, hakan ya haifar da rashin daidaito mai hatsari inda ake dora wa sojoji nauyin aiki fiye da kima, ana karkatar da kasafin kudin tsaro zuwa ayyukan ‘yan sanda na yau da kullum.

Ya tuna cewa a tsarin mulki, manyan ayyukan rundunar sojojin Najeriya sun hada da kare kasa daga farmakin waje, kiyaye cikakken ikon yankuna, dakile tawaye, da bayar da taimako ga hukumomin farar hula idan bukata ta taso.

Sai dai ya jaddada cewa tsaron cikin gida ya kamata a rika jagorantar sa ne ta farar hula tare da dogaro da bayanan leken asiri, inda ‘yan sanda da hukumomin tsaron jiha za su kasance a gaba.

Ya gargadi cewa ayyukan raya kasa da tsaron cikin gida bai kamata su maye gurbin babban aikin sojoji na kare kasa daga barazanar waje ba.

Tun da fari, Ministan tsaro, Janar Christopher Musa, ya yi kira da a dauki mataki na hadin gwiwa domin dakile amfani da hanyoyin sufuri na cikin gida da kungiyoyin aikata laifuka ke yi wajen jigilar makamai, kwayoyi da sauran haramtattun kayayyaki.

Ya bayyana cewa shawo kan wannan kalubale na bukatar shigar kananan hukumomi, sarakunan gargajiya, shugabannin addini da al’umma baki daya, domin aikin tsaro nauyi ne na kowa da kowa, ba na rundunar sojoji kadai ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here