Tun kwanakin baya na Amince da Mafi Karancin Albashi ga Malamai 5,439-Zulum.

Borno
Borno

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya tabbatarwa da shugabannin kungiyar kwadago ta kasa NLC cewa, tuni ya amince da biyan mafi karancin albashi na Naira 30,000 ga malamai Dubu 5 da 439, da suka ci jarabawar cancanta a Hukumar Ilimin bai daya ta Jihar.

Zulum ya bayyana hakan ne a lokacin da jami’an Kungiyar Kwadago karkashin jagorancin Shugaban NLC a Jihar Borno, Kwamared Yusuf Inuwa suka kai masa ziyara, har ma jami’in kwadagon ya godewa Gwamnan bisa jajircewarsa wajen ganin an kyautata jin dadin ma’aikata sannan kuma ya ja hankalinsa ga sauran bangarorin suma a ci gaba da duba halin da suke ciki.

Wata sanarwa ta ce, tantancewar da Zulum ya yi, ya zuwa yanzu an kai ga tantance malamai Dubu 11 da 790, wadanda ba su cancanta ba a tsarin ilimin Jihar Borno amma duk da haka, gwamnan ya ba da umarnin cewa ba za a kori wani ma’aikacin gwamnati ba, sai dai a sake horar da wasu, wasu kuma za a mayar da su zuwa wasu sassan da ba na ilimi ba.

A zaman da ya yi da shugabannin NLC a ranar Laraba, Zulum ya jaddada matsayarsa na kin korar malaman da ba su cancanta ba.

Gwamnan ya shaidawa NLC cewa tun da kwamitin tantancewar ya gano cewa daga cikin malamai Dubu 11 da 790 da aka tantance, akwai malamai Dubu 7 da 975 da basu cancanta ba.

Idan dai za a iya tunawa, tun daga watan Janairun Shekarar 2020, dukkan ma’aikatan gwamnati a matakin jihar, ciki har da malaman makarantun sakandare, suka fara cin gajiyar mafi karancin albashi na Naira 30,000.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here