Tinubu ya kaddamar da sakatariya a jihar Kebbi

IMG 20260214 WA0116 1 720x430

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, kan aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa masu anfani ga al’umma a fadin jihar.

Shugaban ya yi yabon ne ranar Asabar a Birnin Kebbi yayin kaddamar da sabon ginin Sakatariyar Jiha ta zamani da aka sanya masa suna domin karrama shi.

Tinubu ya kuma kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatin Idris ta aiwatar, yana mai cewa kyakkyawan aikinsa bai ba shi mamaki ba.

Ya bayyana Idris a matsayin shugaba mai maida hankali da hangen nesa wanda ke da muradin jama’a a zuciya.

Shugaban ya kuma yaba wa al’ummar jihar kan ci gaba da bai wa gwamnati goyon baya da hadin kai.

Ya ce irin wannan hadin kai ya taimaka wajen nasarorin da aka samu a karkashin jagorancin Idris.

Tinubu ya sake jaddada kudurin Gwamnatin Tarayya na tallafa wa jihohi domin samar da karin ribar dimokuradiyya ga ‘yan Najeriya, musamman a bangarorin more rayuwa, lafiya da ilimi.

Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa NAN ya nuna cewa daga cikin ayyukan da aka kaddamar akwai Babbar Tashar Mota ta Tsakiya ta Birnin Kebbi, wadda aka tsara domin bunkasa harkokin kasuwanci da inganta zirga-zirgar fasinjoji a babban birnin jihar.

Shugaban ya kuma kaddamar da titin Sarki Haruna da aka kara fadada shi zuwa layi uku, Kwalejin Koyon Aikin Jinya da Ungozoma ta Kauran Gwandu da ke Ambursa, da kuma tsohon Argungu By-Pass da aka fadada.

Sabuwar sakatariyar jiha wadda aka fara aikin ta tun 2012, an farfado da ita tare da kammala ta a karkashin gwamnatin Idris, abin da ke nuna kudurin gwamnati na zamanantar da gine-ginen gudanarwa.

Ziyarar aikin ta yini guda ta Shugaban Kasa ta zo daidai da bikin karshe na Bikin Kamun Kifi da Al’adu na Duniya na Argungu karo na 61, inda ya kasance bako na musamman.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here