Jami’ar Bayero ta Kano ta kori ɗalibai sittin bisa zargin aikata laifuffukan satar jarabawa.
Hukumar jami’ar ta bayyana matakin ne ta cikin kundin labaranta na mako-mako da aka fitar a ranar Juma’a, inda aka nuna cewa hukuncin ya biyo bayan nazari mai zurfi kan laifuffukan da aka jingina wa ɗaliban.
Rahoton ya nuna cewa an yanke shawarar korar ɗaliban ne a zaman majalisar dattawan jami’ar karo na 431 da aka gudanar a ranar 7 ga watan Janairu, bayan samun shawarwari daga kwamitocin ilimi da ladabtarwa da suka dace.
Majalisar dattawan jami’ar ta bayyana cewa an same ɗaliban da aikata nau’o’in saba ƙa’idojin jarabawa daban-daban, lamarin da ya sa aka bayar da shawarar korarsu bisa ƙa’idoji da dokokin da jami’ar ke aiki da su.
Hukumar jami’ar ta jaddada cewa ɗaukar irin wannan mataki yana daga cikin ƙoƙarin tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin jarabawa, tare da kare mutuncin takardun shaidar jami’ar.
Jami’ar Bayero ta Kano ta kuma sake nanata aniyarta ta ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai kan duk wani ɗalibi da aka samu da aikata laifin satar jarabawa, domin tabbatar da inganci da sahihancin tsarin karatu da kimantawa a jami’ar.












































